Tarihin ‘Yan Sanda Mata Na Farko A Najeriya

A shekarar 1955, wani muhimmin lamari ya faru a Najeriya – an baiwa mata damar shiga aikin ‘yan sanda a karon farko.

Wani rahoton bidiyo na shekara-shekara yayi bayani game da tafiyar mata ashirin da suka samu horo kuma aka tura su aiki a Legas.

Wannan shirin fim mai suna “‘Yan sandan Mata na farko a Najeriya,” ya dauki tarihin lokacin da rukunin farko na ‘yan sanda mata suka kammala yaye.

Wannan dai wani muhimmin lokaci ne a tarihin Najeriya domin yana nuna shigar mata cikin ‘yan sanda.