Tarihin Tsohon Shugaban Kasar Masar Na Farko, Mohamed Naguib

Mohamed Naguib (1901 – 1984), shi ne shugaban kasar Masar na farko bayan kawo karshen mulkin Masar gargajiya a 1952.

An haife shi a birnin Khartoum na kasar Sudan ga mahaifin shi dan kasar Masar da uwa ’yar Sudan.

Yayi karatu a kwalejin Gordon, sannan ya sauke karatu daga kwalejin soji a shekarar 1918. Ya sami digirin digirgir a shekarar 1927, inda ya zama kwararren sojan Masar na farko da ya samu digirin digirgir. Daga baya ya samu digirin shi na biyu a fannin siyasa a shekarar 1929.

Ya zama Birgediya Janar a 1948, kuma shugaban farko a 1952 bayan ayyana jamhuriyar.

Yayi murabus a shekara ta 1954, kuma magajin shi Gamal AbdelNasser ya tsare shi a gida har zuwa shekara ta 1971. Daga nan ne shugaban kasar Anwar Sadat ya sake shi, amma ya kasance a karkashin shi har zuwa mutuwar shi a shekara ta 1984 a lokacin mulkin Hosny Mubarak.

Shugaba Naguib ya kasance mai karfin imani da gudanar da mulkin farar hula kuma ya biya makudan kudade saboda kiraye-kirayen da ya yi na mika mulki ga zababbun fararen hula da kuma hafsoshin soji don komawa barikokin su.