Tarihi

Tarihin Shigowar Hanyar Sadarwa Tarho A Najeriya

A sama hoton wani Basaraken Arewa ne yayin da yake waya a Kano a shekarar 1937, bayan da Alexander Graham Bell ya kirkiri wayar tarho a shekarar 1876, kuma bata dauki lokaci mai tsawo ba ta yadu a duniya.

An sanya wayar tarhon farko a Najeriya, wadda a yanzu ake kiranta da Najeriya, a Legas a shekarar 1886. A shekarar 1893, wayar tarho ta zama abin da ake amfani da ita a kusan dukkan ofisoshin mulkin mallaka na Legas.

Daga Legas kuma aka karasa zuwa Ilorin sannan kuma zuwa Jebba a farkon karni na ashirin. Sannan zuwa Calabar da Kano.

Advertisement