Tarihin Masarautar Biu A Borno Da Sarakunan Ta
Sarakunan Biu sun fara ne da Abdullahi, wanda aka fi sani da Yamta-ra-Wala ko Yamta Mai Girma, wanda ya kafa mulkinsa a shekara ta 1535. A zamanin Mari Watila Tampta a wajajen 1670 ne aka san Biu a matsayin masarauta. Babban kabila a Biu su ne ’yan kabilar Babur/Bura, wadanda suke da alaka da kabilar Kanuri.
A cewar almara, wanda ya kafa Biu ya fito ne daga wani wuri, ya ci babban garin da ke yankin, sannan ya kafa sabon babban birni a Dlimbur, wanda a yanzu ya zama wurin binciken kayan tarihi. Zuriyarsa ta kafa dauloli biyu masu gaba da juna, daya a Kogu daya kuma a Mandaragirau da ke kusa.
A zamanin Sarki Mari Watirwa (1793-1838) na Kogu, an fatattaki Fulani mahara daga Masarautar Gombe zuwa yamma. A shekarar 1878, Mari Biya ya zama sarkin Bura na farko da ya fara sarauta daga Biu, kuma fadar sarki tana cikin garin.
A shekarar 1918, da zuwan Turawan mulkin mallaka na Biritaniya, aka kirkiro sashen Biu. An karrama Mai Ari Dogo a matsayin Sarkin Biu na farko a shekarar 1920. Yankin ya samu sunan daular Biu ne bayan da aka kara masarautun Shani da Askira a shekarar 1957.
Masarautar Biu ta kunshi kananan hukumomin Biu, Hawul, Kwaya Kusar, da Bayo. A al’adance masarautar Biu ta kasance tana samar da Mataimakin Gwamnan Jihar Borno mai wakiltar Kudancin Jihar. Har zuwa kwanan nan, akwai masarautu uku a jihar Borno: Masarautar Borno, Masarautar Dikwa, da Masarautar Biu.
Sai dai a watan Maris din shekarar 2010, Gwamna Ali Modu Sheriff ya raba tsohuwar Masarautar Dikwa zuwa sabuwar Masarautar Bama da Dikwa. Wannan shawarar ta kai ga gabatar da koke daga mutanen Hawul, Kwaya Kusar, da Bayo, wadanda su ma suna son sarakuna daban-daban.