Tarihin Manjo-Janar Muhammadu Buhari

An haifi janar Muhammadu Buhari mai ritaya tsohon shugaban mulkin soji na Nigeria a birnin Daura na jihar Katsina a ranar 17 ga watan Disamban 1952, ya kuma aure Safinatu Yusuf a shekara ta 1971, inda har ma suka haifi yaya hudu.

Janar muhammadu Buhari mai ritaya ya halarci makarantun Primary a birnin Daura da kuma Mai Aduwa a tsakanin shekarun 1948 zuwa 1952.

Ya kuma halarci makarantar Middile ta Katsina a tsakanin 1956 zuwa 1961 ,daga nan ne kuma ya shiga makarantar horas da soji dake Kaduna a shekara ta 1962.

Janar tsohon shugaban mulkin sojin dai na Nigeria Buhari, ya halarci makarantar horas da aiyukan soji Aldershot dake kasar Birtania a tsakanin 1962 zuwa 1963, daga nan kuma sai ya wuce zuwa horas da soji ta Wellington.

Ya kuma halarci makarantar da horas da dabarun yaki ta Amurka a shekara ta 1979 zuwa 1980, lokacin ne aka baiwa Buhari mukamin 2Nd Lieutenet a shekara ta 1963.

Janar muhammadu Buhari mai ritaya ya taba zama kumandan bataliya ta biyu dake karkashin dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar dikin duniya da aka tura zuwa jamhuriyar demorcadiyar Congo a lokacin da take amsa tsohon sunanta na Zaire.

Buharin dai ya taba rike mukamin gwamnan mulkin soji na jihar Borno a shekara ta 1975 zuwa 1976.

Janar Buharin dai ya rike mukamai da da dama na soji tare kuma da samun lambobin yabo na duniya gida da waje kafin kuma a nada shi kann mukamin shugaban mulkin soji na Nigeria a ranar daya ga watan Janairun 1984, bayan da soji suka karbi mulki daga hanun gwamnatin farar hula ta shehu shagari, kafin kuma daga bisani soji suka sake kwace mulki daga hanun Buharin a ranar 27 ga watan Agustan 1985,tun daga wanan lokacin ne aka tsare shi, kafin kuma sako shi a ranar 13 ga watan Disamban 1988.

A shekarar data 2004 ne dai janar Buhari mai ritaya ya shiga cikin harkokin siyasa kace kace,inda har ma ya tsaya takarar neman shugabancin Nigeria a wasu zabuka da aka yi a Nigeria karkashin jama’iyarsa ta ANPP, inda suka tsaya takara neman shugabancin Nigeria shi da shugaba Olusegun Obasanjo, zaben kuma da Buharin bai sami nasarar lashe shi ba.