Asalin Maguzuwa Da Alaƙar Su Da Hausawa A Yau
Mutane da dama sun daɗe su na da wata tambaya a zuciyar su a kan su waye Maguzawa?
A wannan labarin za mu bayyana ko su waye Maguzawa, kamar yadda wani marubuci kuma manazarci Ibrahim Aminu Daniya, ya habarta wa kafar yada labarai BBC Hausa.
Su dai Maguzawa mutane ne Hausawa da yawancin su manoma ne kuma suna a ƙauyukan ƙasar Hausa.
Malam Ibrahim ya bayyana cewa, mutane ne masu ƙwazo da ƙoƙarin aiki tukuru, sai dai yawancin su ba addinin Musulunci suke bi ba, kamar waɗanda suke tare da su a yankunan da suke, amma daga baya sannu a hankali wasu daga cikin maguzawan na shiga Musulunci.
Ya ƙara da cewa, al’adun su da yaren su, da kuma sutura sun dace da na Hausawa musamman kafin jihadin Shehu Ɗan Bin Fodio, kuma su na nan birjik a wurare da dama musamman kamar wasu ƙauyuka a jihar Kano da jihar Katsina.
Abin da aka fi karkata a kai na tarihi a cewar masanin shi ne, mutane ne waɗanda suka zo daga ƙasa Habasha (Ethiopia) tun ana kiran:su ‘Majusu,’ suka riƙa sauya suna har aka dawo ana kiran su Maguzawa a yau.
Da yawan masu tarihi na ganin cewa maguzawa su ne asalin Hausawa daga baya suka samu ilimi suka zama Hausawan da muka sani a yau.
Sai dai masanin yace, daga baya an samu sabani, domin wasu na ganin cewa alama ta fi nuna cewa muguzawa mutanen Afrika ta arewa ne, domin al’adar da ta fito daga nan irin wacce suke yi, kafin su dawo arewacin Afrika, kamar Najeriya, Nija, Kamru da sauran su.
“Akwai mutanen da suka zo daga Habasha suka zauna a Dutsen Dala da ke Kano, kuma mashahurin sarkin su shi ne wani da ake kira (Barbushe), waɗannan mutane sun riƙa bautar wasu alloli saɓanin (Ubangiji), su kuwa maguzawa da aka sani a yau ba su bautar komai, amma su na da nasu abubuwan na tsafe-tsafe.”
Har yanzu dai, ba a san maguzawa da wani harshen da suke magana da shi ba in ba yaren Hausa ba.
In Da Aka Fi Samun Maguzawa
Manazarcin yace, an fi samun maguzawa a ƙasar Hausa musamman a dazukan Kano da Katsina, akwai su suna nan amma sannu a hankali su na shiga cikin jama’a su na karɓar Musulunci, don haka, yanzu ƙalilan ne suka rage daga cikin maguzawan.
Ya kara da cewa, wasu daga cikin al’adun maguzawa da suka yi kama da na Hausawan da suka rungumi Musulunci a yau sun haɗa da na; Bukukuwan aure ko na mutuwa, da kaɗe-kaɗe, wake-wake da raye-raye.
“Sunayen maguzawa sun sha bambam da na Hausawa, domin su su na sanya sunaye ne dai-dai da yanayi ko lokacin da ake ciki.
Misali idan yanayin roron wake ne sai su sanya wa mutum suna ‘Ci Wake,’ ko idan lokacin damina ne sai su sanya wa yaro suna ‘Damina,’ ko su sanya sunayen Aljanu saboda su ne abokan mu’amalar su akai-akai, musamman wajen bori da sauran su.
Marubucin ya cigaba da cewa, a yanzu dai babu wani ƙiyasi na adadin yawan maguzawan da suka rage a ƙasar Hausa, abin da kawai yake a fili shi ne, yawan maguzawa ya ragu sosai, kuma yana cigaba da raguwa domin yawanci sun haɗe da sauran jama’a yadda in ba sun faɗa ba, ba za ka gane cewa su maguzawa ne ba, don haka akwai yiwuwar wata rana maguzawan za su ƙare ɗungurungum, saboda sun bace cikin al’ummar Hausawa.