Tafoki Na APC Ya Lashe Kujerar Majalisar Wakilai Ta Kankara

Hon. Shehu Dalhatu Tafoki, dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya lashe zaben cike gurbi na dan majalisar tarayya mai wakiltar Kankara/Faskari/Sabuwa a jihar Katsina.

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana Tafoki a matsayin wanda ya lashe zaben a hukumance bayan ya samu kuri’u 49,807 inda ya kayar da jam’iyyar PDP, da dan takararta, Hon. Jamilu Lion, wanda yazo na biyu da kuri’u 49,067.

Raba sakamakon zaben da kananan hukumomi suka yi kamar yadda rahotanni suka ce INEC ta gabatar kamar haka.

Karamar hukumar Kankara: APC – 16,758, PDP – 22,360

Karamar hukumar Faskari:
APC – 22,711, PDP – 19,347

Karamar Hukumar Sabuwa: APC – 10,338, PDP – 7,360

Sakamakon gaba daya ya nuna yadda APC ke da rinjaye, inda ta samu kuri’u 49,807 idan aka kwatanta da kuri’u 49,067 na PDP.