Taƙaitaccen Tarihin Wasan Fulani Da Kanuri ‘Barebari’
Akasarin Barebari wato Kanuri da Fulani ba su san tarihin wasan da ke tsakanin su da juna ba, illa dai kawai sun tashi sun ga iyayen su da kakannin su su na wasan zolayar juna idan sun gamu.
Wasan da ke tsakanin Barebari da Fulani tarihi ya nuna cewar, bunƙasar shahararriyar Daular Borno ta Kanuri ta soma yin ƙasa ne tun bayan rasuwar sarki, Mai Idris Aloma, a wajan ƙarni na Goma Sha Bakwai. Don haka, ya zamana daular ta dinga asarar manyan garuruwan da suke ƙarƙashinta sakamakon yadda ƙarfin ikon ta yake durƙushewa.
A cikin wannan yanayi ne sai kuma Fulani suka fara yin jihadi a shekarar Alif da Ɗari Takwas da Huɗu miladiya (1804), don haka ne, bayan yaƙe-yaƙen su ya yi ƙamari sai ya zamana su na tashi zuwa garuruwa domin cin su da yaƙi wanda har sai da ta kai har Masarautar Borno sun riska da yaƙi.
A shekarar Alif da Ɗari Takwas da Takwas (1808) ne Fulani suka ƙwace cibiyar Masarautar Borno da ke garin Gazar, inda aka yi gurmuzu suka cinye tare da ƙone garin da kuma korar mayaƙan garin.
A shekarar Alif da Ɗari Takwas da Goma Sha Huɗu (1818), Babban malami a Daular Borno mai suna, Shehu Muhammadul Amin El-kanemi, ya jagoranci kafa sabuwar daular Borno a wani gari mai suna Kokawa, sannan ya haɗa runduna gami da soma taimakon sarkin su mai suna, Mai Dunama Na Fiyafi, daga baya-bayan sarki Mai Dunama ya so hallaka Shehul Muhammadul Amin El-kanemi saboda farin jinin shi a wajen jama’a, amma bai samu nasara ba, sai shehu Muhammadul Amin ya zamo sarkin Borno mai cikakken iko ba tare da zubda jini ba.
Don haka, ya shiga ƙalubalantar Fulani da suka hana su sakat ta hanyar yaƙar su da kuma aikewa da wasiƙun ilimi ya na tuhumar shugaban Fulani, Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo, a kan cewa, “Don me zai shiga yaƙi da Daular Borno alhalin ta fi shekaru Ɗari Takwas da karɓar addinin Musulunci, kuma da sunan yaƙin Musulunci?”
A haka dai aka dinga gwabzawa da yaƙi da kuma rubuce-rubuce na wasiƙu har zuwa rasuwar Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo. Yayin da ɗansa, Muhammadu Bello, ya gaje shi.
A shekarar Alif da Ɗari Takwas da Ashirin da Shida (1826), in da yaƙi ya ƙara ƙamari a tsakanin su, babu jimawa kuma bayan kowa ya sha kaye a hannun ɗan uwan shi, sai kuma aka yanke shawarar yin maslaha, a nan dai aka yi salhu aka bar Kanuri wato (Barebari) da birnin su, amma dai sun rasa ikon wasu yankuna da a baya suke hannun su izuwa hannun Fulani
Yadda aka yi wasan ƙabilu ya shiga shi ne ɗirkakowar mayaƙin nan daga ƙasar Sudan zuwa yankin Borno, wato Rabe Zubair Ibini Fadlallah, a cikin shekarar Alif da Ɗari Takwas da Casa’in da Uku.
Rabe, ya zo daga Sudan da shirin gaske ya afkawa Daular Borno da yaƙi, nan da nan ya yi ƙarin kumallo da ita Rabe da mutanin shi abin da suka ga dama suke yi a Borno.
A wani yaƙi da aka yi a kusa da Borrno ne sojojin Faransa na mulkin mallaka suka kashe Rabe bayan ya yi mulki a shekaru Bakwai da watanni Bakwai da kwanaki Bakwai. Bayan lokaci kaɗan kuma, Ingia suka ci ƙasar da yaƙi suka mayar da zaman lafiya da salama.
Wuyar da Kanuri suka sha a hannun Rabe wanda ya zamo ba su sha a yaƙin suka yi da Fulani ba, shiyasa Fulani suke tsokanar su idan sun gan su da cewar; “Ga Rabe nan.”
Su kuwa Barebari sai ka ga sun hargitsa kamar Ɓera ya hango Kyanwa. Daga baya kuma da Barebari suka gane cewa, tsokana ce kawai, sai suke mayar da martani har kuma abin ya zamo wasan tsokana tsakanin waɗannan ƙabilun guda biyu, amma dai har izuwa yau Ɓarebari sun yarda su sanyawa ƴaƴansu sunan Usman, amma ba sa sanya wa ƴaƴan su sunan Rabe ko kuma Rabi’u.