Tarihi

Sunan Fatakwal Na Farko Kafin A Canza Shi A Shekarar 1913

Fatakwal babban birnin jihar Ribas ne a kudancin Najeriya, sannan kuma shine birni na biyar mafi girma a Najeriya bayan Legas da Kano da Ibadan da kuma Kaduna.

Yan Najeriya da dama sun san birnin da Fatakwal, amma kadan ne daga cikin su suka san tsohon sunan birnin, wanda kuma a halin yanzu ake kiran birnin.

Birnin Fatakwal ya kasance yana da sunan “Iguocha”, wanda sunan “Ikwerre” ne wanda aka samo daga kalmar Igbo “Ugwu Ocha” (Farin Tudun). Sai dai da aka kafa tashar ruwa a birnin, wadda aka kafa da nufin fitar da gawayin da aka gano a Enugu, a karkashin gwamnatin Lord Fredrick Lugard ta mulkin mallaka, sabuwar tashar ta bukaci a yi suna.

Saboda haka, kamar yadda Vanguard ta ruwaito, a cikin watan Agustan 1913, Gwamna Janar na Najeriya na lokacin Sir Fredrick Lugard, ya rubuta wasiƙa zuwa ga sakataren mulkin mallaka na lokacin (Lewis Vernon Harcourt), cewa duk da cewa ba za su iya samun sunan yankin da ya dace ba ga sabuwar tashar jiragen ruwa, cikin girmamawa zai nemi izinin shi don a kiram sabon tashar jiragen ruwa Port Harcourt.

Sakataren Gwamnati ya ba da izinin shi, kuma ta haka ne birnin da aka fi sani da “Iguocha” ya zama sunan Fatakwal.