Suka Dimka: Mutumin Da Ya Jagoranci Juyin Mulkin Da Ya Kai Ga Mutuwar Murtala Mohammed

Juyin mulki a Najeriya ya kasance wani muhimmin bangare na tarihin Najeriya, kuma watakila za a iya cewa tushen matsalar Najeriya ba yau aka fara ba, amma ana iya gano ta a wani lokaci da ba a yi nisa ba.

Buka Suka Dimka wani hafsan sojin Najeriya ne wanda ya taka rawa a juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatin Murtala Muhammed a ranar 13 ga Fabrairun 1976. Dimka ya kuma halarci juyin mulkin Najeriya na 1966 wanda ya hambarar da gwamnatin Aguiyi Ironsi.

Laftanar Kanar Buka Suka Dimka ya kasance jigo a juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekarar 1976 inda aka kashe shugaban kasar Najeriya Janar Murtala Muhammed. Da ya gane cewa juyin mulkin bai yi nasara ba, sai ya gudu zuwa Afikpo da ke Jihar Anambra a lokacin, ya nemi mafaka tare da wata tsohuwar budurwa.

Hagu – Dimka : Murtala – Dama

Nan take bayan kashe shi, sai ya garzaya zuwa gidan radiyon Najeriya NBC domin bayyana nasarar juyin mulkin wanda bai sani ba har yanzu bai yi nasara ba. An kama shi ne a watan Maris, 1976. A watan Mayun 1976 Dimka da wasu masu yunkurin juyin mulki shida an kashe su a bainar jama’a ta hanyar harbi da bindiga a gidan yari da ke Legas.