Kuna Yin Minshari Yayin Barci? Wannan Maganin Naku Ne

Idan kuna Saraga yayin barci , waɗannan maganin shine zaku gwada.

Minshari ko Saraga wani abin kunya ne kuma mummuna amo ko kara da ake yi yayin barci. Ya raba masoya da yawa saboda Saraga wani abu ne da ba shi da sauƙin sarrafawa yayin barci.

Wadannan sinadarai na gargajiya zasu taimake ka ka warkar da Saraga in Allah yaso.

Sinadaran:
Tuffa/Apple 2.
kKaras 2.
Lemun tsami ko lemun zaƙi 1½.
Sanyun Tafarnuwa 1.

Haɗawa:
A wanke dukkan sinadaran, a yayyanka su zuwa kananan girma kuma a jujjuya su zuwa blender don niƙa. Ku ci sa’o’i kadan kafin barci kowane dare.

Bayan wasu makonni ko watanni za ku sami yanci gaba ɗaya daga wannan maƙarƙashiyar da ke damun abokin tarayya da dare.

Wannan ruwan ya’yan itace yana da tasiri saboda abubuwansa. Vitamic C na lemun tsami yana tsaftace hanyoyin hanci.