Tarihi

Seychelles: Ƙasar Da Yawan Al’ummar Ta Basu Kai Mutum Dubu 100 Ba

Nahiyar Afirka tana da kasashe sama da 50 kuma jimillar al’umma ta kai biliyan 1.3 bisa ga cikakken bayani daga Worldometer.

Najeriya tana da yan kasa sama da miliyan 200, a halin yanzu ita ce kasa mafi girma a Afirka wajen yawan al’umma.

Yayin da kasar Afirka ta yamma, Najeriya na iya zama sananna ga yawan al’ummar ta, akwai wata kasa a yankin gabas mai nisa na Afirka da aka sani da karancin al’ummar ta.

Seychelles kasa ce dake tsibirin Gabashin Afrika mai kunshe da tsibirai 115. Kasar dai tana gabashin gabar tekun Somaliya ne kuma kasar Burtaniya ta ba ta yancin kai a watan Yunin 1976, kimanin shekaru 46 da suka gabata.

Bisa cikakken bayanin da aka yi bitar yawan al’ummar duniya, Seychelles na da kimanin mutane dubu 99 (99,426) a shekarar 2022.

Wannan bai kai adadin mutanen kowace jiha a Najeriya ba.

Seychelles tana addini sosai, inda kashi 89.2 na al’ummar kasar Kiristoci ne, kashi 1.6 cikin dari Islama, da kuma Hindu kashi 2.4.

A halin yanzu Seychelles tana karkashin jagorancin Wavel Ramkalawan, dan siyasar Seychelles kuma limamin cocin Anglican wanda ya karbi mukamin shugaban kasa a watan Oktoba 2020.

Babban birnin kasar, Victoria yana da yawan mazaunan dubu 26, kuma shi ne birni mafi girma a Seychelles.