Tarihi

Sarakunan Gargajiya 3 Da Suka Yi Aikin Soji A Najeriya Kafin Hawan Sarauta

Sarakunan gargajiya sune aka fi sani a yankin Arewacin Najeriya. Wasu daga cikin wadannan sarakunan gargajiya na Arewa sun yi abubuwan hidima kafin su hau karagar mulki. Wasu ‘yan kasuwa ne, ‘yan siyasa, har ma da tsoffin ma’aikata masu hidima.

Haka nan kuma akwai wasu daga cikin wadannan sarakunan gargajiya na Arewa da suka yi aikin sojan Najeriya kafin su yi ritaya suka zama sarakunan garinsu.

A kasa akwai wasu sarakunan gargajiya na Arewa da ke karkashin wannan fanni.

1. Sarki Yahaya Abubakar: Shi ne Etsu na 13 a yankin Nupe a jihar Neja. Ya zama sarkin masarautarsa ne a ranar 11 ga watan Satumbar 2003 bayan ya gaji kawunsa, Alhaji Umar Sanda Ndayako, wanda ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya.

Kafin nada shi Sarkin Nupe, Yahaya ya yi aikin sojan Najeriya na tsawon shekaru 28 kafin ya yi ritaya a shekarar da ya zama Sarkin Nupe. Ya yi ritaya da mukamin Birgediya Janar na Sojojin Najeriya.

2. Muhammadu Sa’ad Abubakar: Shine Sarkin Musulmi na 20. An nada shi Sarkin Musulmi ne a ranar 6 ga watan Nuwamba 2006 bayan ya gaji dan uwansa kuma tsohon Sarkin Musulmi Muhammadu Maccido wanda ya rasa ransa a hatsarin jirgin sama a Abuja.

Kafin nadin sa, Sa’ad Abubakar ya yi aikin sojan Najeriya na tsawon shekaru 31 kafin ya yi ritaya da mukamin Birgediya Janar na sojojin Najeriya.

3. Mohammed Sani Sami: Shine Sarkin Zuru na yanzu a jihar Kebbi. Kafin ya zama Sarkin Zuru, Sani Sami ya yi aikin sojan Najeriya na tsawon shekaru bayan ya shiga aikin soja a watan Disambar 1962.

Ya kuma kasance gwamnan soja daga Janairu 1985 zuwa Agusta 1985, lokacin mulkin soja Muhammadu Buhari. Kafin ya zama Sarkin Zuru, ya yi ritaya daga aikin sojan Nijeriya da mukamin Manjo Janar na Sojojin Nijeriya a shekarar 1990.

Sani Sami ya yi aikin sojan Nijeriya na tsawon shekaru 28.