Sabuwar Wayar Huawei Mate 60 Pro
Huawei Mate 60 Pro ita ce wayar da ta girgiza duniya a wannan wata, amma duk haka wasu mutane suna yada farfaganda akan iPhone 15 wacce ga dukkan bayanai ba wani sabon abu da tazo da shi da sauran wayoyin iPhone da suka gabata.
Idan za’a yi tunawa, an hana kamfanin Hauwei amfani da Android OS da sauran operating system akan kayan su, sai suka kirkiri nasu nauyin system mai suna Harmony, har ila yau, aka sake hana su amfani da Chip na sauran wayoyi, sai suka samar da nasu chip din mai dauke da 5G network mai suna (Kirin 9000s).
Sabuwar wayar Hauwei Mate Pro tana da karfin yin Satellite call, wanda haka ke ba masu amfani da ita damar yin kira hatta a cikin ruwa.
Ta kowane bangare sabuwar wayar Hauwei Mate 60 Pro tafi sabuwar wayar iPhone 15, kamar yadda masana suka bayyana.
- Camera: 3 (50 MP + 48 MP + 12 MP)
- Battery: 5000 mAh
- Storage: 256GB/512GB
- Ram: 12GB