Ruwan Dafin Kunama: Ruwa Mafi Tsada Da Amfanin Su

Abubuwan mamaki basa karewa a wannan duniya, kuma wani abu mafi bada mamaki shi ne ruwan dafin kunama yana iya kai dalar Amurka miliyan $39 galan ɗaya.

Ruwan dafin kunama ya zama wanda shi ne ruwa mafi tsada a duniya. Ana bukatar digon ruwan dafin kunama miliyan 2.64 domin a cika galan guda.

Dafin kunama yana da nau’ikan magunguna da dama a cikin sgi, tun daga cututtukan daji zuwa maganin zazzabin cizon sauro.

Yawancin bincike sun nuna ruwan dafin kunama yana da tasiri a matsayin mai rage radadi ko zafin ciwo da kuma maganin cututtuka irin su lupus da ciwon gaɓoɓi.

Yanzu, masu bincike a Jami’ar Stanford da kuma Mexico sun gano cewa kunama da ake samu a Gabashin Mexico tana da dafin da zai iya samar da sinadarankashe kwayoyin cuta.