Lafiya

Yadda Zaku Kare Kan Ku Daga Ƙuragen Fuska

Fitowar kuraje a fuska da ake kira da (Pimples) a turance, na daya daga cikin ababen da ke bata kwalliyar mace.

Wasu kurajen duk hodar da aka sanya musu, ba ta iya boyar da su a lokacin kwalliya saboda tsabagen girmansu. Shi ya sa na kawo muku yadda za a bi domin kare fuskarmu daga fitowar kuraje ta hanya mai sauki.

Kamar yadda ake cewa rigakafi ya fi magani. A samu zuma mai kyau sai a hada ta da ruwa sai a sha kullum da safe domin samun fatar fuska mai santsi.

Ko kun san cewa turara fuska da ruwan dumi na kore miyagun kuraje daga fitowa?

Turara fuska na bude ramukan gumi wadanda suka toshe domin gumi da kuma dauda. Idan gumi da dauda suka toshe ramukan fitar gumi a fatarmu, sai ya zama maiko wanda zai haifar da fitar kurajen fuska.

Haka zalika, turara fuska na taimaka wa jinin jikinmu wucewa ba tare da bata lokaci ba.

Domin, hanyoyin su zama a tsabtace don gyara fuskar. Za a iya turara fuska a gida. Yadda ake turara fuska A tafasa ruwa a tukunya sai a hada ta da ganyen ‘thyme’ da ruwan lemun tsami. Bayan ruwan ya tafasa, sai a sauke shi daga wuta.

Sai a rufe kai da tawul domin turirin ruwan ya turara fuskar amma a dan yi baya da robar ruwan zafin kadan domin kada a kone. Turara fuska sau daya a mako na kare fuska daga fitowar miyagun kuraje. .

Advertisement