Tarihi

1983: Mutumin Da Ya Shirya Juyin Mulkin Da Ya Kai Buhari Ga Karagar Mulki

An haifi Sambo Dasuki a ranar 2 ga Disamba, 1954, a Jihar Kaduna, ga iyalan Alhaji Ibrahim Dasuki. Ya taba zama mai baiwa shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin tsaro da kuma Muhammadu Buhari a takaice.

Sojoji karkashin jagorancin Manjo Janar Muhammadu Buhari sun hambarar da gwamnatin farar hula ta tsohon shugaban kasa Shehu Shagari a karshen shekarar 1983. Juyin mulkin shi ne na biyar bayan samun yancin kai a shekarar 1960, inda sojoji suka mamaye babban birnin Legas.

Majiyar Premiumtimesng.com ta ruwaito Sambo Dasuki (wanda a lokacin Manjo ne) kuma mataimaki ga Janar Mohammed Inuwa Wushishi ne ya dauki nauyin juyin mulkin da Najeriya ta yi a shekarar 1983 wanda ya kai Manjo Janar Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya.

A juyin mulkin da aka yi a watan Disambar 1983, Dasuki tare da wasu hafsoshin soja guda biyu sun yi tattaki zuwa Jos domin yiwa Manjo Janar Buhari bayani, wanda a lokacin shi ne GOC na runduna ta 3 da ke rike da makamai a kan cigaban shirin juyin mulkin 1983 wanda yasa Buhari ya zama babban wanda ya ci gajiyar shirin kawar da zababben shugaban kasa Shehu Shagari.

Dasuki a lokacin da yake rike da mukamin mai bai wa kasa shawara kan harkokin tsaro a gwamnatin da ta shude, ya kara karfafa tare da ba da damar fadada rundunar hadin gwiwa ta Multi-National Joint Taskforce (MNJTF) tare da kasashen Benin da Kamaru da Chadi da Nijar da ke makwabtaka da kasar domin yakar yan ta’addan Boko Haram.