Lafiya
Mutum Na Farko Da Aka Taɓa Yiwa Dashen Zuciyar Alade Ya Mutu
Wani Ba’Amurke wanda shine mutum na farko a tarihi da aka taɓa yiwa dashen zuciyar alade ya mutu.
Ya rasu ne bayan watanni biyu bayan gwajin da aka yi masa, asibitin da yayi aikin tiyatar ya sanar da mutuwar a ranar Laraba.
A cewar asibitin, mutumin mai shekaru 57 da haihuwa, David Bennett, ya mutu ranar Talata a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Jami’ar Maryland dake Amurka.
Likitoci, ba su bayyana ainihin musabbabin mutuwar mutumin ba, inda suka ce yanayin shi ya fara tabarbarewa kwanaki da yawa a baya.