Mustapha Na APC Ya Lashe Zaben Cike Gurbi Na Sanatan Yobe Ta Gabas

A ranar Lahadin da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Musa Mustapha a matsayin wanda ya lashe zaben cike gurbi na sanatan Yobe ta Gabas.

Mataimakin shugaban jami’ar gwamnatin tarayya ta Gashua, FUGA, Ibrahim Ahmed Jajere, jami’in zabe, ya bayyana cewa Mustapha ne ya samu kuri’u mafi yawa.

Jajere ya ce dan takarar APC ya samu kuri’u 68,778 inda ya kayar da abokin hamayyarsa Aji Kolomi na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 18,878.

Jami’in zaben ya bayyana cewa, jimillar kuri’un da aka kada sun kai 90,949, inda aka samu sahihan kuri’u 88,771, yayin da kuri’u 2,178 suka ki amincewa.

“Ni, Mataimakin Farfesa Ibrahim Ahmed Jajere, a nan na tabbatar da cewa ni ne Jami’in kula da takarar neman kujerar Sanatan Yobe ta Gabas na 2024 da aka gudanar a ranar 3 ga Fabrairu.

“An fafata a zaben kuma Musa Mustapha na APC ya samu kuri’u 68,778; Aji Kolomi na PDP ya samu kuri’u 18,878.

“Musa Mustapha na APC bayan ya cika sharuddan doka an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara kuma an dawo da shi zaɓaɓɓe,” in ji shi.

Mustapha, wanda aka fi sani da Coolers, ya kasance tsohon kwamishinan kudi na jihar Yobe.

Zai maye gurbin Sanata Ibrahim Geidam, wanda ke rike da mukamin ministan harkokin ‘yan sanda.

Cikakken sakamakon zaben kamar haka.

1) Bursari LG

*APC – 9,466

*PDP – 2,752

2) Damaturu LG

*APC – 11,941

*PDP – 6,693

3) Geidam LG

*APC – 6,621

*PDP – 2,310

4) Gujba LG

*APC – 11,529

*PDP – 3,037

5) Gulani LG

*APC – 12,516

*PDP – 2,198

6) Tarmuwa LG

*APC – 5,557

*PDP – 1,054

7) Yunusari LG

*APC – 11,148

PDP – 834