Kimiyya

Mene Ne Gas Ɗin “CNG ” Da Amfanin Shi?

Akwai wani Gas da ake kira CNG ‘Compressed Natural Gas’, wanda yafi Fetur arha, ya fi shi sauƙin mu’amulla, haka zalika ana amfani dashi amadadin fetur ko dizel.

Ƙasashen da basu da man fetur irin su Sri Lanka sun jima da shi suke amfani, a motocin su, da injinan su da sauran al’amuran yau da gobe. Wani ɓangare na India da Pakistan suna amfani da shi sosai. A Canada birnin Calgary da America duk ana amfani da wannan gas duk da kasancewarsu masu arzikin man Fetur.

Shi wannan gas baya saka mota hayaƙi, kuma bashi da haɗarin tayar da gobara kamar fetur ko gas na girki, don bai kai iska nauyi ba. Kuma ana siyar dashi N230 per ‘SCM’ (standard cubic meter), wanda zaka iya fada da gwari-gwari kace irin cylinder 12kg (ita ce a ƙaramar mota) dai-dai take da zuba mata 14SMC ya cika ta.

Kuma akan farashi N3,212. Kuma zaka iya tafiyar 150km zuwa 180km sannan zai ƙare. Idan kuma a cikin gari zakayi yawo zakayi tafiyar kimanin 100-120km sannan gas ɗin N3212 zai ƙare.

Wani abin sha’awa ko da kana tafiya sai gas dinka ya ƙare ko zai ƙare, kana danna botton akan dash board ɗinka motar zata koma kan fetur idan kana dashi ta cigaba da aiki.

Adadin ‘Natural gas reserve’ ɗin da Nigeria take dashi yafi adadin man fetur ɗin da muke dashi sau 3 (5,300 km3 (187×1012 cu ft)), don haka abu ne mai ɗorewa tunda ta hanyar kamfanin ‘Nigeria Liquefied Natural Gas’ ake tura shi ƙasashe daban daban ta jirgin ruwa.

Anan Arewacin Nijeriya bamu da CNG, amma a jihar Edo da Ogun tun shekarar 2007 ake amfani da wannan gas, kuma motoci sama da 10,000 a yanzu haka suna aiki da wannan gas din. Karamin misali shine ka lura da manyan motocin Dangote a tsakanin kan su da Tankinsu zaka ga wasu cynlinders manya guda 2, to CNG ne a ciki, kuma motocin da shi suke aiki, suna shan kimanin na N124,000 so zo daga Birnin Legas ko kudancin Nijeriya.

Aikin AKK pipeline da Gwamnatin Shugaba Buhari ta fara a Kano shine hanya mafi sauƙi da za’a iya kawo wannan gas jahohinmu na Arewa, kasancewar ba za’a iya dakon ɗauko shi abiyo mota dashi ba yana CNG, sai dai a ɗauko shi a LNG sannan a samar da abinda zai iya mayar dashi CNG anan arewa. Wannan dogon karatu ne.