Meroe: Inda Ake Binne Bayi Da Ransu Tare Da Sarki Idan ya Mutu A Masar

A shekara ta 1836 CE, wani maharbi dan Italiya yayi bombin saman mafi yawan rufi na Meroe don neman zinariya.

A ƙarshe ya sami zinariyar, amma a lokacin, mutanen ƙasar sun yi fushi da shi har ya gudu don tsira da ran shi.

Kamar yadda bincike ya nuna, an binne sarakuna bakaken fata ‘Firaunoni’ (Pharoahs) a nan tare da bayi (waɗanda ake binne su da rai don yi wa sarakuna (Fir’auna) hidima a lahira) da dawakai, da karusai, da zinariya da sauran abubuwa masu daraja waɗanda wataƙila sun yi yawa a cikin daular a lokacin da ta yi girma.

Bayan baturen Italiya ya rusa ganuwar don neman zinariya

Sarakunan ko Sarkin ƙasar Masar ana kiran shi da suna ‘Fir’auna’, ba, ko Fir’auna wanda yayi lokaci tare da Annabi Musa Alaihissalam shima shima sunan lakabi ne na sarakunan Masar.

A cikin karni na 8 BC, wani wanda ake kira shab’ka, yana mulki daga nan, ya mamaye Masar kuma ya kafa daular da ta tashi daga Khartoum na zamani zuwa Iskandariya.

Daular ta bunkasa. Dakarun Musulunci ne za su rufe shi a shekara ta 650 Miladiyya. Babu shakka kogin Nilu ya cigaba da mulkin daular.

Wani jami’in sojan Burtaniya ya rubuta wannan na kogin Nilu; “Rayuwar wannan kasa ce da ta ke bi ta cikinta, in ba kogi ba, da babu wanda ya fara, ba tare da shi ba, da ba wanda ya cigaba. -Winston Churchill.