Masu fama da cututtuka 17, ko fiye da hakan makamantan wadanda muka lissafa a kasa, zasu nemi rake mai kyau mai zaki sai a yayyanka ta gunduwa-gunduwa, sannan a saka lita ɗaya ta ruwa a saka danyen citta a ciki kwara daya, sannan a tafasa su sosai.
Za’a basu lokaci mai tsawo sai sun tafasa iya tafasa, sai a sauke su daga kan wuta a saka lipton kadan da ake bukata. Lipton ɗin yana fara jika za’a cire shi, domin ba’a son yayi yawa sai a lura da kyau.
Haka zalika, kada a saka suga, haka ma zuma, kada a kara komai a ciki fiye yadda muka bayyana.
Wannan haɗin magani ne mai fa’ida sosai ga lafiyar jikin ɗan adam.
Ga jerin magungunan a kasa:
- Mura
- Tarin Sanyi
- Tarin Tsufa
- Tarin Huhu
- Ciwon Hakarkari
- Tarin Asma
- Tarin Nimoniya
- Majinar Kirji
- Majinar Ciki
- Majinar Kunkuru
- Yawan Atishewa
- Ciwon Kirji
- Sanyin Jiyoji
- Sanyin Ruwa
- Ciwon Gabobi
- Kaikayin Ido/Kunne
- Ciwon Makogwaro
A kula: Muna gargadin cewa idan mutum yana fama da wasu rashin lafiyoyi masu sarkakiya ya kamata ya tuntubi likita kafin amfani da wannan magani.