Maganin Sanyin Mata Mai Sanya Warin Gaba, Fitar Farin Ruwa Da Kuraje
Idan mace na fama da wadannan matsalolin kamar haka to ta jarraba wannan maganin inshaa Allahu za ta samu waraka.
1. Matsanancin ciwon sanyin mara.
2. Kananan kuraje da ke fitowa a gaban mace in ana jima’i da ita sai ta rinka Jin zafi kamar gaban zai tsage.
3. Mace mai fitar farin ruwa a gaban ta.
4. Mace mai warin gaba.
5. Mace mai yawan ciwon mara duk lokacin al’adar ta.
Duk macen da ke fama da wadannan matsalolin to ta nemi:- KANWA Cokali 3, GISHIRI Cokali 2 da TAFARNUWA dunkule 1.
Sai ta zuba ruwa dai-dai adda zai kai ta shiga cikin baho ta zauna, sai ta dafa shi inya dahu sa ta juye shi a baho, in ya ‘dan sirace sai ta shiga ciki ta zauna, na tsawon minti goma zuwa shabiyar sannan ta fita daga ciki.
To lallai zata sha mamakin yadda za taga cutar sanyi ke fita a gaban ta, sannan in tana son ya zama ta rabu da wa’dancan matsalolin gaba daya, to sai ta lara da wannan kuma bayan tayi wancan na farkon.
Ta nemi:
1. MAN ZAITUN kwalba 1.
2. MAN TAFARNUWA kwalba 1.
3. MAN KWAKWA kwalba 1.
Sai ta hada su a kwano daya ta soya su, amma za ta soya ne da TAFARNUWA Dunkule 1, in ya soyu sai ta sauke shi ta bar shi ya huce (yayi sanyi sosai) sai ta juye a roba, sannan ta nemi auduga sai ta sa sawa audugar wancan mayi sai juku da mayin sannan sai ta dauka ta sanya ta a gaban ta, ba za ta cire ba har sai bukatar fitsari ko bayan gida ta taso mata, sannan sai ta cire.
Lalle mace in ta jarraba wannan za ta sha mamakin yadda za ta ga wani mummunan abin da zai fita abjikin ta na cuta, sannan za ta ga tana gitar da wani yellown ruwa a gaban ta ko ta ga wani bakin ruwa yana fita in ta zo fitsari to alamar sanyin ya fita a jikin ta kenan kwata-kwata.