Maganin Cutar Sikila Na Gargajiya

Ciwon sikila cuta ce ta kwayoyin halitta ta ciki jini wacce ke tattare da jajayen kwayoyin halitta marasa kyau wadanda ke daukar siffar sikila. Wannan yanayin ciwon idan ya tashi zai iya haifar da ciwo mai tsanani, lalacewar gabobin jiki, har ma da mutuwa da wuri a wasu lokuta.

Kananan yara sune wadanda suka fi shan wahalar cutar sikila. Manyan alamomin cutar sikila ga ƙananan yara sun haɗa da; kumburin gaɓoɓin jiki, mummunan raɗaɗi, rashin lafiya akai-akai da ba a gane kansa ba, da yawan ƙonewar jini da zarar sun ɗan yi ƴar karamar rashin lafiya kamar zazzaɓi.

Sai dai kuma har yanzu babu wani hakikanin maganin cutar sikila a likitance. Duk da haka wannan baya nufin cewa cutar bata da magani sam-sam, domin dukkan Musulmi sun yi imanin cewa “Allah ubangiji bai saukar da wata cuta ba, har sai da ya saukar da maganin ta, kamar yadda yazo a wasu littattafan Musulunci da dama.

Saboda da haka, a yau zamu yi bayanin yadda za’a yi maganin cutar sikila ko saukake ciwon ta hanyar amfani da haɗin magungunan Muslunci ko (gargajiya).

Yadda za’a haɗa maganin cutar sikila shine za’a samu nonon shanu mai tsafta da kuma man zaitun mai ingantacce.

Za’a rika hada nonon shanun da man zaitun ɗin ana baiwa mara lafiya tun da safe kafin ya ci wani abinci. Hakan za’a ci gaba da yi har zuwa tsawon wani lokaci ko da alamun cutar sun kau.

Insha’ Allah, wannan maganin zai taimaka sosai ga masu fama da irin wannan lalurar rashin lafiyar mai hadari.

Amfanin Nonon Shanu Da Man Zaitun

Nonon shanu yana cike da muhimman sinadirai kamar calcium, phosphorus, bitamin B, potassium da bitamin D. Plus, yana da kyakkyawan tushen furotin. Shan nonon na iya hana osteoporosis da karyewar kashi har ma da taimakawa wajen kula dukkan jiki.

Man zaitun kuma yana cike da kitse masu lafiya ga zuciya da kuma antioxidants, yana mai da shi karin girma ga abinci mai gina jiki.

Haka nan an danganta man zaitun da jerin fa’idodi masu tsawo kuma yana iya kariya daga kumburi, cututtukan zuciya, kansar nono, da nau’in ciwon sukari na 2.