Tarihi

Mace Ta Farko Da Aka Taɓa Buga Hoton Ta Akan Kuɗin Najeriya

Muna da matan Najeriya da dama da gwamnati ta karrama saboda hazakar su a baya da yanzu. Daya daga cikin wadannan matan ita ce Ladi Kwali wacce sunan ta ne aka buga a kan takardar Naira Ashirin ta Najeriya.

Ladi Kwali ta kasance yar Najeriya mai fasaha, kuma mai sana’ar tukwane wadda ta yi suna a kasar tun tana karama. Ta zama ma’aikaciyar tukwane tun tana ƙuruciyar ta bayan innar ta, ta horar da ita wadda ita ma babbar mai tukwane ce.

An gano gwanintar ta a shekara ta 1950 bayan da masu fada a ji a cikin gida suka fara baje kolin ayyukan ta kuma manyan mutane da yawa sun gano ta.

A shekarar 1954, Kwali ta samu karbuwa a kasar bayan ta shiga Cibiyar Pottery Center ta Abuja, kuma ta zama mace ta farko a Najeriya da ta samu horo kan fasahar tukwane.

Saboda hazakar da take da ita, Ladi ta fara karatu a wasu Al’ummomi kuma ta samu karbuwa a wasu Kasashe ciki har da Turai.

A cewar jaridar The Guardian, gwamnatin Najeriya ta yanke shawarar karrama ta ne ta hanyar buga hoton ta a kan kudi naira ashirin ₦20,na Najeriya inda ta zama mace ta farko kuma tilo da aka buga hoton ta a takardar kudin Najeriya.

A cewar Wikipedia, an kuma sanya mata sunan wata babbar hanya a Najeriya. Ladi ta rasu a ranar 12 ga Agusta, 1984.