Labarin Ɗan Wani Dattijon Wata Ƙabila Da Manyan Gari Bayan Rasuwar Mahaifin Shi

Wani dattijo mai hikima ya mutu kuma ya bar yaro karami, wanda bai isa ya shugabanci kabilar ba. ’Yan uwa sun fafata ne don neman shugabancin, amma sun kasa daidaita kan wanda za su zaba.

Suka je wurin alkali ya yanke hukunci a tsakanin su.

Alkalin yana son gwada hankalin su, saboda haka ya ba kowannen su kofin shayi ya ce musu: ku mayar da kofin fanko, kuma kada ku sha shayin ko ku zubar a ƙasa. ‘

Mutanen duk a rude suka kalli juna ba su san yadda ake yi ba. alkali ya nemi a kawo yaron dan wannan dattijon da ya rasu, sai kuma ya umurci yaron da abin ya umarci mutane farko.

Yaron ya zarce duk dattijai, ya dauki guntun tsumma, ya nutsa a cikin kofin shayin har sai da ya shanye duka kofi.

Yaron ya ce wa alkali: ‘kofin ka ya zama fanko.

Alƙali ya fahimci wayon yaron, sai ya cewwa duk mutanen: ‘Ku tashi ku ɗauki sabon shugaban ku.’

#Afrika #Hikima