Dalilin Da Zai Sanya Ka Daina Cin Indomi Da Sauran Dangogin Shi Sosai

Duk abincin da aka tace sosai ba zai taɓa kasancewa mai kyau ga lafiyar dan Adam ba, musamman idan muna yawan cin abinci kamar Indomi akai-akai ba, saboda Indomi yana ɗaya daga cikin abincin da mutane ke ci akai-akai a duk faɗin duniya, musamman a nahiyar Afirka.

Wannan saboda, ana ɗaukarsa azaman abinci mai saurin girkuwa, wanda za’a iya shirya shi cikin sauƙi a kowane lokaci. To, yana da mahimmanci mu san illar dake tattare da wannan abincin.

Saboda haka, muka yi wannan dan gajerin bayani ya akan dalilin da ya kamata mu rage cin abinci Indomi akai-akai.

Babban dalilin da ya sa ya kamata mu rage hakan shine saboda suna daya daga cikin abincin da aka sallatar, ma’ana amfanin shi ga lafiya yayi kasa mutuka.

Irin waɗannan abinci suna ɗauke da sinadarai waɗanda ke da ikon yin illa ga lafiyarmu da saninmu ko ba tare da saninmu ba. Indomi yana da wasu daga cikin waɗannan sinadarai waɗanda aka tattauna a nan.

Indomi ana yin su ne da sinadarai kamar su monosodium glutamate (MSG), additives, preservatives da butyl hydroquinone waɗanda ba su da fa’ida ga kiwon lafiya.

A maimakon haka, cin su sau da yawa yana haifar da cututtuka masu haɗari kamar cututtukan koda, matsalolin hanta da dai sauransu waɗanda za su daɗe kuma yana iya haifar da mutuwa idan ba a kula da su yadda ya kamata ba.

Ga abinda wani likita yace akan wannan batun:

Yawan cin abinci mai sinadaran sodium na iya ƙara haɗarin hawan jini wanda zai rikide zuwa wasu cututtuka kamar matsalolin koda, matsalolin zuciya, bugun jini da sauransu.

Bugu da ƙari kuma, wani dalili shi ne saboda Indomi ba su da matakin sinadaran fiber na abinci kuma suna da ƙarancin sinadaran furotin. Suna dauke da kitse kuma tarin wannan kitse a jiki yana iya haifar da cututtuka kamar kiba, yawan cholesterol, matsalolin ciki da sauransu.

A ƙarshe, gidaje da yawa a yau ba za su iya zama ba tare da suna da Indomi a cikin ɗakunan dafa abinci su ba.

Dole ne mu lura da haɗarin shan waɗannan abinci akai-akai don ceton lafiyarmu.