Kabilar Bodi: Al’ummar Da Babban Ciki Shine Adon Su

Kabilar Bodi ta kasar Habasha (Ethiopia)sun shahara da gargajiya da al’adunsu na musamman, kuma daga cikin abubuwan da suka fi ban mamaki shi ne yadda maza ke fafatawa da samun kiba da babban ciki domin lashe gasa a ƙauyukan su.

Al’ummar sun jima suna kallon wannan al’adar a matsayin wata alama ta nuna kyau, ado da daraja a cikin yan ƙabilar, kuma mazan suna daukar tsauraran matakai don tabbatar da cewa suna da manyan ciki.

Mazan al’ummar sukan bi wasu hanyoyi masu tsauri da suka haɗa da shan ruwan jinin saniya da madara ba tare da dadi ba, kuma sau da yawa hakan kan sa su rashin lafiya.

Wanda ya lashe gasa ta baya-baya

An yi imanin cewa wannan cakuden jini da madarar shanu yana da sifofin sihiri wanda ke bada damar cikin mutum ya girma zuwa girman babba, kuma mazan suna son yin kasadar shan shi don a gan su a matsayin mafi kyau ƙauyen su.

Wannan al’ada ce mai ban mamaki kuma mai ban tsoro da aka yi ta shekaru aru-aru, kuma da wuya ta canza nan da jimawa.