Kimiyya

Jihar Farko Da Jirgin Sama Ya Fara Sauka A Najeriya

Harkokin sufurin jiragen sama ya zama sananne sosai a cikin shekarun da suka gabata. Mutane da yawa sun fi son yin tafiya ta jirgin sama domin ba ya ɓata lokaci. Ya kamata a ce akwai filayen tashi da saukar jiragen sama da yawa a fadin jahohi 36 na Tarayyar Najeriya.

A wani rahoto da jaridar Premium Times ta wallafa, jirgin na farko ya sauka a tarayyar Najeriya a shekara ta 1925. Yana da kyau a yi nuni da cewa har yanzu Najeriya na karkashin turawan ingila ne a daidai wannan lokaci. Mu kalli jaha ta farko da jirgin sama ya sauka a tarayyar Najeriya.

Jihar Kano

Wannan jiha tana cikin Tarayyar Najeriya. Jihar Kano tana da matsayi mai matukar muhimmanci a tarihin tarayyar Najeriya.

A cewar rahoton da Premium Times ta fitar, jirgin na farko ya sauka a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.

Jihar Kano ta ci gaba da zama daya daga cikin jahohin da ake mutuntawa a Tarayyar Najeriya.