Kimiyya

Pantami Ya Kaddamar Da Mota Mai Aiki Da Lantarki Da Aka Kera A Najeriya

Ministan Sadarwar Najeriya Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami, ya ƙaddamar da Motar farko da aka fara ƙerawa a Najeriya.

Ministan yayi gwajin motar lantarki wadda kamfanin (Hyundai Kona) suka kera a Najeriya jim kadan bayan ya karbi bakuncin Hukumar Kula da Kera Motoci ta Kasa (NADDC) karkashin jagorancin shugaban hukumar Darakta Janar Jelani Aliyu a ziyarar aiki.

Tawagar NADDC ta kasance a cibiyar sadarwa da Tattalin Arziki na Dijital dake Abuja don bincika haɗin gwiwa tare da ma’aikatar a fannonin fasahar Dijital da cigaban Abubuwan cikin gida.

Kera motar lantarki ta farko a duniya;

A cikin 1832, Robert Anderson ya haɓaka motar lantarki ta farko, amma sai a shekarun 1870 ko daga baya cewa motocin lantarki sun zama masu amfani.

Akwai motar lantarki da wani ɗan ƙasar Ingila ya gina a 1884. Hoton Smithsonian.