Tagullar Benin Da Aka Wawashe Shekaru 100 Da Suka Wuce An dawo Da Su

An maido da tagulla biyu na masarautar gargajiyar Benin a Najeriya, fiye da karni daya bayan da sojojin Birtaniya suka yi awon gaba da su, lamarin dake kara sa rai cewa za’a iya mayar da wasu dubban kayayyakin tarihi zuwa gidan kakannin su.

Masu bincike da masu mulkin mallaka ne suka sace kayayyakin tarihin, galibi a Turai, daga Masarautar Benin, a yanzu kudu maso yammacin Najeriya, kuma suna cikin manyan abubuwan tarihi na Afirka.

An kirkire su a farkon karni na 16, a cewar gidan kayan tarihi na Biritaniya.

A wani gagarumin biki da aka yi a birnin Benin a ranar Asabar din da ta gabata don nuna dawowar wani hoton zakara da shugaban wani sarki Oba (sarki), mai magana da yawun fadar Charles Edosonmwan yace an kwashe wasu daga cikin tagulla zuwa New Zealand da Amurka da Japan.

Jami’ar Aberdeen da kuma Kwalejin Jesus ta Jami’ar Cambridge ne suka mika kayayyakin tarihi guda biyu ga babbar hukumar Najeriya a watan Oktoba, amma har yanzu ba su koma gidan kakannin su ba.