Tarihi

Usman Katsina: Babban Janar Ɗin Sojojin Najeriya Na Farko Daga Arewa

Hassan Usman an haife shi a shekara ta 1933 a jihar Katsina, daga ajin mulkin Fulani. Ya kasance dan mai martaba Sarkin Katsina Alhaji sir Nagogo.

Ya fara makaranta tun yana dan shekara 7 a makarantar firamare ta Kankiya. Bayan ya kammala karatu ya shiga aikin sojan Nijeriya a shekarar 1956. Shi ne Gwamnan soja na farko a rusasshiyar yankin Arewa.

Gwamnatin Katsina, ta ga tsananin kyamar Igbo, wanda yasa a shekarar 1966 na kin jinin Igbo, garuruwa da dama sun yi kaca-kaca da kashe-kashe da dama a sakamakon juyin mulkin da yayi sanadin mutuwar Firimiya Ahmadu Bello.

Daga baya ya zama babban hafsan hafsoshin soji, daga baya kuma ya zama mataimakin hafsan hafsoshin soji, hedikwatar koli a karkashin gwamnatin Janar Yakubu Gowon. A lokacin yakin basasa, ya jagoranci yakin ta hanyar ninka sojojin, tare da toshe kayan abinci ga Biafra. Ya shaida mika wuya na Biafra ga Najeriya ba tare da wani sharadi ba. Janar Hassan Usman yayi ritaya daga aikin soja a matsayin babban gogaggen hafsan soja.

Mutum ne mai rikon amana, ya rasu a shekara ta 1995, dan talaka duk da kasancewar shi Gwamna a duk fadin yankin Arewa ya bar gida uku kacal, daya daga cikin gidan da aka ce kyauta ce ta dace da mutum-mutumin shi. Ya mutu bai bar wani abin jin daɗi ba ga ‘ya’yan shi. Amma ya bar musu gado mai kyau sosai, yana mai fayyace cewa: “Sunan kirki ya fi dukiya”.