Lafiya

Yadda Za’a Magance Matsalolin Ciwon Hanta Cikin Sauki

Don Girman Allah ku turawa sauran yan uwa domin su amfana.

Ciwon hanta ya zama ruwan dare inda yake kara yaduwa a bainar jama’a.

Ga wata fa’ida wanda masu fama da wannan ciwon zasu iya jarrabawa domin samu waraka daga lalurar cikin nufin Allah.

Abubuwan da za’a samu;

• Ganyen Zogale busashshe.

• Yayan Baure ko garin yayan busashshe.

Sai a hade waje guda a dake su suyi laushi,mai fama da Matsalar ya rika shan karamin chokali a nono kuma madara ta ruwa ko kunu sau 2 a rana.

Don kada ku manta da sharing zuwa ga yan uwa da abokan arziki domin su amfani da wannan maganin.

Allah ya bamu lafiya da dukkan Musulmi.