Fa’idodin Ganyen Na’a-Na’a Wajen Kashe Kurajen Fuska Da Gyaran Fata

Ganyen Na’a-Na’a shima yana da nashi amfanin mai yawa sosai wurin gyaran fata da sa jiki yayi laushi domin yana da wasu sinadarai masu tsaftace fata kamar yadda masana kimiyya suka tabbatar.

Yadda za’a hada: A samu ganyen Na’a-Na’a a markada shi, bayan anyi haka, sai a shafe fuska da hannu da kuma jiki, sai a bar shi yayi minti 10 zuwa 15, sannan sai a wanke.

Shi wannan ganyen yana kashe kuraje, batar da bakaken tabo dake fuska, da kuma yana laushin fata da kyau.