Fadar Etsu Nupe: Daɗaɗɗen Tarihin Sarauta Da Masarautar Nupe

Fadar Nupe, wacce aka fi sani da fadar Etsu Nupe, wuri ne da ya kamata duk mai sha’awar tarihin masarautar Nupe ya gani.

Gidan da ke birnin Bida a jihar Neja a Najeriya, an gina shi ne a farkon karni na 19, kuma shi ne wurin mulkin Etsu Nupe, sarkin gargajiya na kabilar Nupe.

Etsu Nupe Na 13, Yahaya Abubakar a cikin fadar shi.

Gidan sarautar wani tsari ne mai ban sha’awa wanda aka gina shi na farko daga laka ne, sannan aka sake samfarin ginin da kayan gine-ginen zamani kuma an ƙawata shi da zane-zane masu ba sha’awa.

A cikin fadar, baƙi za su iya bincika ɗakuna daban-daban, tsakar gida, da baranda waɗanda suka haɗa da tsarin. A halin yanzu, akwai kuma ɗakin karatu mai cike da takardu na tarihi da kayayyakin tarihi na Masarautar Nupe, da kuma wani gidan tarihi da aka keɓe don tarihin masarautar.

Farfajiyar fadar Etsu Nupe, Yahaya Abubakar da sauran mutane tare da fadawa.

Bugu da ƙari, akwai wuraren bukukuwa da yawa da ake gudanar da bukukuwan gargajiya da na al’ada, wanda ke ba wa baƙi damar samun hanya ta musamman a cikin tarihin sarauta da al’adu na Masarautar Nupe.

Fadar dai wani muhimmin bangare ne na kayan tarihi na yankin kuma ta zama wajibi ga duk mai sha’awar al’adun mutanen Nupe.