Dalilin Da Yasa Wasu Mata Ke Sake Ɗaukar Ciki Ƴan Makonni Bayan Haihuwa

Ciki a cikin mata ba wai kawai yana haifar da sauye-sauyen yanayi ba, canjin abinci mai gina jiki, da sauye-sauyen jiki, amma kuma yana shafar yawancin ayyukan su na yau da kullum. Sakamakon yadda akasarin mata sukan fuskanci yanayi iri-iri a lokacin daukar ciki, akwai wasu matan da ba sa son daukar ciki na tsawon makonni da dama bayan sun haifi sabon jariri.

Da farko dai, wannan shi ne saboda ba su da shiri a hankali don shiga cikin zafi da rashin jin daɗi da ke tattare da ciki da haihuwa.

Duk da haka, yana yiwuwa sababbin uwaye su kasance masu ciki a cikin ‘yan makonni da haihuwa, koda kuwa wannan shine sakamakon da suke tsammanin samun mafi ƙarancin damar faruwa da su.

Sakamakon wadannan abubuwa, mace na iya daukar ciki bayan makonni kadan da haihuwa, kamar yadda mujallar lafiya Healthline ta bayyana.

Rashin Shayar Da Jariri Nono

A baya-bayan nan ne kwararru a fannin likitanci suka gano cewa macen da ta haihu amma ba ta fara shayarwa ba nan take ba, to tana matukar hatsarin ɗaukar ciki a cikin makonni shida na farko bayan haihuwa. Baya ga wannan bayanin, an nuna cewa ovulation na iya farawa tun makonni shida na farko bayan haihuwa a wasu mata, koda kuwa macen ba ta shayar da yaron ta.

A wannan lokacin, mace ta fi saurin samun juna biyu idan ta sami saduwa (jima’i) ba tare da wata kariya ba tare da wani mutum da ake ganin “mai iya haihuwa ne.”

Don hana yiwuwar yin ciki a cikin makonni masu zuwa bayan haihuwa, Healthline ta ba da shawarar amfani da hanyoyin saka tarar haihuwa kamar; Pills, Allurar Depo da saka Robar kariya ga damtsen hannu.

Ku tuntubi likatan ku kafin ɗaukar wani mataki.