Dalilin Da Yasa Mutumin Da Ya Ƙirkiri AK-47, Yayi Takaicin Ƙirƙira Ta Kafin Ya Mutu

Laftanar-Janar Mikhail Kalashnikov wani janar na Rasha ne, mai ƙirƙira, injiniyan soja, kuma mai ƙirar ƙananan makamai wanda ya ƙirƙiri Ak-47 mai ban tsoro da muka sani a yau.

A lokacin yaƙin duniya na biyu ne ya ƙirƙiro bindigar AK-47 mai hatsarin gaske ba tare da tunanin cewa ita ce makamin mafi ƙarfi na zaɓi ga ƴan daba, ƴan ta’adda, da masu mulkin kama karya a duk faɗin duniya ba.

Kafin mutuwar Mikhail Kalashnikov a shekara ta 2013, ya rubuta wasiƙar damuwa ga shugaban Cocin Orthodox na Rasha cewa: “Har yanzu ina cigaba da yin wannan tambayar.

“Idan bindiga ta ta yi sanadin mutuwar mutane, kuma ni mai bin Cocin Orthodox ne nake da laifin mutuwar su, ko da kuwa makiya na ne?