Tarihi

Dalilin Da Yasa Ƙasashen NATO Ba Zasu Yaɓa Barin Yukiren Ta Faɗi Ba

Ya zuwa yanzu, babu wani taimakon soja kai tsaye daga kasashen NATO ko Majalisar Dinkin Duniya a Ukraine. Wadannan kasashe dai sun kakaba wa Rasha takunkumin karya tattalin arziki ne kawai domin gurgunta ko kuma hana shugaba Vladimir Putin kara kai hari kan cibiyoyin soji a Ukraine. Wannan ba yana nufin Amurka da kawayenta za su kyale sojojin Rasha su kame kasar gaba daya ba saboda za ta kafa tarihi mai hatsari a fagen siyasar duniya, kasuwanci da huldar bangarori daban-daban.

Idan kasashen yammacin duniya suka gaza kare Ukraine daga ci gaba da kai hare-hare, babu wata kasa da za ta yi marmarin kulla alaka mai mahimmanci da kasashen kawancen NATO. Hakan kuma zai samar da karin damammaki ga kasashen Rasha, China da sauran kasashen ketare domin gano karin kasashe masu son keta takunkumin da kasashen yammacin duniya suka kakaba mata.

Ukraine da kasashen Yamma suna jin daɗin dangantakar juna wanda dole ne a dore. Tun bayan barkewar yakin, gwamnatin Amurka ta ba da taimakon kudi na miliyoyin daloli, Firayim Ministan Burtaniya Boris Johnson ya kuma sanar da ba da taimakon kudi ga Ukraine. Duk da haka, gwamnatin Ukraine ta nemi karin makamai ba tare da fitar da su ba.