Tarihi

Dalilin Da Yasa Aka Jefa Gawar Osama Bin Laden A Cikin Teku

Osama Bin Ladin yayi kaurin suna a shekarar 2011 da wata tawagar sojojin Amurka na musamman da aka fi sani da Seal Team shida suka kashe.

Mutane da yawa sun kasa yarda cewa gwamnatin Amurka ce ta kashe shugaban na Al Qaeda a karkashin jagorancin shugaban kasar na wancan lokacin, Barack Obama amma da lokaci ya kure, ba su da wani zabi illa su yarda cewa an harbe shi. An binne Usama nan take a cikin teku.

A cikin wannan rubutu, zan fara bayanin dalilin da ya sa aka binne Usama a teku ba a cikin kabari a kasa ba:

Da a ce an binne Usama a kasa, da mutane sun mayar da kabarinsa wata cibiyar sha’awa kuma masu biyayya gare shiya zasu yi yaki ba tare da gajiyawa ba domin su kwato gawar shi.

Jami’an Amurka a wata hira da aka yi da su sun ce da ba zai taba yiwuwa wata kasa ta amince da binne gawarsa ba kasancewar yana da babban laifin kashe mutane da dama, don haka yana da kyau a binne gawarsa a teku.

Har ila yau, da yawancin ‘yan ta’adda da suke da alaka da shi, zasu yi amfani da kabarinsa a matsayin mafaka ga masu kishin Islama, duk da cewa addinin Musulunci ya haramta.

Ba a saba yin binne a cikin teku ba a cikin addinin Musulunci ko wasu addinai, amma ana iya barin shi a wasu yanayi. Alal misali, idan wanda aka kashe ya mutu yayin da yake cikin jirgin ruwa kuma zai ɗauki kwanaki kafin su isa ƙasa don jana’izar.

Haka kuma, an yi ta rade-radin cewa an binne shi ne a cikin teku domin ba shi ne ainihin Osama Bin Laden ba, amma rahoton DNA ya nuna cewa Osama ne aka kashe aka binne shi a teku.