Dalilin Da Yasa Aka Cire Yakubu Gowon Daga Karagar Mulki A 1975

Watanni biyu gabanin cikar shi shekaru 32 a ranar 19 ga Oktoba, 1966, Yakubu Gowon ya hau mulki a matsayin shugaban Najeriya na uku, wanda ya zama shugaban kasa mafi karancin shekaru.

Wasu kananan hafsoshin sojin kasar sun kori Janar Yakubu Gowon a wani juyin mulkin da sojoji suka yi ba tare da zubar da jini ba a Najeriya a ranar 29 ga Yulin 1975.

Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban Najeriya, yayi ikirarin cewa rashin cika alkawarin da Yakubu Gowon yayi na cewa za a wargaza mulkin sojoji nan da shekara ta 1976, shi ne muhimmin abin da ya haddasa faduwar Gowon.

Tsawon zaman shu a matsayin shugaban mulkin soja a Najeriya ba a taba ganin irin shi ba a baya. Gowon yayi shekara tara a matsayin shugaban kasa.

Murtala Mohammed, wani karin babban kwamandan soji ne ya bi shi a matsayin magajin shi. Lokacin da aka yi juyin mulkin, ya tafi birnin Kampala na kasar Uganda, inda ya halarci wani taro da kungiyar hadin kan Afrika ta shirya.