Lafiya

Dalilai 5 Da Zasu Sanya A Riƙa Cin Cucumber Akai-Akai

Cucumber ƴaƴan itace ne da aka saba amfani da su azaman kayan lambu.

Ana iya amfani da Cucumber don haɗa abinci masu yawa. Cucumbers galibi launin kore ne kuma suna da ɗanɗano mai daɗi, wannan shine dalilin da yasa mutane da yawa ke son sa.

Wadannan ƴaƴan itacen yana da fa’ida mai yawa ga lafiyar jiki wanda yana kyau a ci shi cikin daddare.

1. Yana hana ƙishirwa: Jikinmu yana buƙatar ruwa don yin aiki yadda ya kamata kuma cucumbers ya ƙunshi ruwa 96%. Wannan yana taimakawa wajen hana mutum rashin ruwa bayan motsa jiki ko lokacin zafi. Hakanan, isassun ruwa a jiki yana iya hana mashaƙo da tsakuwar koda.

2. Yana dauke da sinadarin antioxidants: Cucumbers yana dauke da antioxidants da flavonoids. Wadannan sinadaran suna taimakawa wajen toshe oxidation wanda zai iya haifar da cututtuka na kullum kamar ciwon daji.

3. Yana taimakawa wajen rage kiba: Cucumbers na iya taimakawa wajen rage kiba saboda karancin kuzari. Hakanan yana ƙunshe da kaso mai yawa na ruwa wanda zai iya haifar da rage nauyi. Kuna iya cin cucumbers da daddare saboda basu ƙunshi adadin kuzari waɗanda zasu iya haifar karin kiba ba.

4. Yana taimakawa wajen fitar bayan gida: Lokacin da kuke cin cucumber da daddare, kuna iya samun motsin hanji da safe. Wannan shi ne saboda cucumber yana da yawan ruwa kuma yana dauke da fiber wanda ke da amfani ga hanji kuma yana taimakawa wajen hana kumburin ciki.

5. Yana magance warin baki: Cin cucumber da daddare na iya rage warin baki da safe. Warin baki yakan faru ne lokacin da kwayoyin cuta ke cin abinci a cikin baki. Sai dai ruwan da ke cikin cucumber yana taimakawa wajen wanke baki daga kwayoyin cutar da ke haifar da warin baki.