Dalilai 2 Da Zaka Iya Cin Goro Domin Su
Kwayar Goro ita ce ƴaƴan itacen ‘Kola Nut’ na Yammacin Afirka. Bishiyoyin suna samar da ƴaƴan itace mai waɗanda muka saba gani, wanda ya kai tsayin ƙafa 40 zuwa 60.
Ana iya samun Goro iri biyu zuwa biyar a kowane duƙulen Kola Nut. Wannan ƙananan ƴaƴan itace, kuma yana da yawan Caffeine.
Idan aka tauna, kwayayen ‘Kola Nut’ suna da ɗanɗano mai tsauri. Dadi yakan canza idan sun bushe, sai a ce suna warin goro.
A cewar MedicalNewsToday, ga dalilai guda hudu da ya sa za ku riƙa cin Goro a kowace rana.
1. Yana Rigafi Da Magance Ciwon Daji: An nuna cewa Goro yana da amfani wajen magance cutar kansar prostate (Prostate Cancer) a cikin bincike da dama.
2. Yana Taimakawa Wajen Maganin Mura/Majina: Tauna Goro na iya taimakawa wajen maganin mura ta hanyar kawar da cunkoson hanci, da taimakawa wajen zubar da jini, da magance ciwon makogwaro, da dai sauran su.