Cututtuka 15 Da Tumfafiya Ke Warkarwa A Jikin Ɗan Adam

Ita wannan bishiyar, mutanen da suka gabata a shekarrun baya su suka fi amfani da ita wajen maganin wasu cututtuka a zamanin su.

Sai dai a wannan lokacin amfani da tumfafiya dan yin magani ya ragu sosai ganin akwi karamcin wannan bishiyar a kasashen da suke da kimiyar binciken tasirin bishiyoyi da tsirran itatuwa a duniyar magani. Sun fi maida hankalin su ga ire-iren bishiyoyin da suke da su a kasashen su.

Bayanin yana da yawa za mu yi kokari na takaitawa dan masu bukata su karanta su amfana shi ne manufar mu.

1 – Saiwar tumfafiya ana amfani da ita ga wanda maciji ya ciza.

2 – Ana amfani da bawon tumfafiya ko itatuwan, waton stems (sanyu) a turance kenan dan maganin cutar kuturta (leprosy). Za’a dake itatuwan a nemi man kade a kwaɓa sai a shafa a inda cutarta ta bayyana.

3 – Ana cin kwallon dake a cikin furen tumfafiya. Idan aka bude fulawar za’a ga wannan dan kwallon a cikin furen tumfafiya to shi za’a ci ba dukkanin fulawar ba. Yana maganin kamin mugu waton mayu kenan, saboda ba su qaunar ruhi da jinin mai cin furen tumfafiya.

Idan zaku lura, zaku ga akwi wata fara da ake samu ga tumfafiya kadai mai launin kore. Ita wannan farar bata da abincin da ya wuce wannan fulawa ta tumfafiya. Ita ma magani ce sosai na karya sihirin maye da maitar shi.

4 – Ana gauraya bawon bishiyar tumfafiya da garin habbat sai a turare ko wane lungu ko daki, ko gida ko duk wani waje da ake bukata. Wannan na korar baqaqen iskoki da miyagun qwari kamar macizzai da makamantan su.

5 – Ana gauraya garin ganyen tumfafiya dana lalle a kwaɓa a shafa a inda ciwo yake. Yana maganin cututtukan cin ruwa, tsagewar yatsa da ciwon yatsa na dan kakarai.

6 – Mai tarin fuka na asthma, ya nemi ɓawon tumfafiya ya shanya su bushe ya cinna masu wuta yayi tirare.

8 – Tsutsar ciki, a nemi furen a yi blending a tafasa a tace ruwan a tarfa zuma kadan a sha.

9 – Basir mai tsiron da ya fito a dubura kuma ya ki komawa kuma yana zubar da jini, a nemi ganyen tumfafiya kwara biyu ko uku a kara a wuta su dan yi zafi kadan sai a shafa man Vaseline a saman ganyen a danne duburar kan inda basir din yake zai koma nan take, inshaa Allah.

10 – Ciwon jiki na shawara, a tafasa ganyen da shi da fatar ayaba a tsaye ruwan a yi wanka da su safe da yamma.

11 – Cututtukan fata kamar kurajen jiki, qaiqayi da sauransu, a nemi man kade sai ka sanya madarar nan ta tumfafiya a gauraya da kyau a rika shafawa bayan an yi wanka. Anti fungal ne mai karfi.

12 – Yana rage yawan faduwa na farfadiya, sai a nemi saiwar da ɓawon a shanya su bushe. A nemi karin bayani domin rubutun nada yawa.

13 – Wanda wani ɓangare na jikin shi ya mutu ko yake gab da mutuwa (paralysis) to a nemi ɓawon
a shanya su bushe, a nemi kitsen damo sai ayi amfani da shi.

14 – Cizon kare, sai a yi blending na ganyen sai ya marmasa gishiri ciki a tafasa a rika wanke wajen da cizon yake.

15 – Ciwon baki dana hakora a tafasa ganyen da shi da fatar lemun tsami sai a marmasa gishiri a rika wanke baki da su.

Cututtukan ciki da hanta a tafasa a tarfa zuma mai kyau a sha.