Bayanin “Tecno Spark 8P” A Taƙaice

Kamfanin da ya kera wayar Tecno Spark 8p Series ko kadan basu ja baya a kasuwar wayoyin zamani ta Afirka ba; ƙira mai inganci da fasaha + farashi mai araha.

Tecno ya yanke shawarar amfani da hanyar SIRI don sakin Tecno Spark 8P a wannan lokaci.

A matsayin wacce ke bima Tecno Spark 7P, Tecno Spark 8P yana ba da ingantaccin abubuwa musamman tare da girman kyamara da sauran su.

4GB na RAM, 64GB memori na sararin ajiya akan wayar, baturi mai girman 5000mAh, nunin pixels 1080 x 2408, da mai sarrafa octa-core da ke aiki a 1.8 GHz, ya riga ya bayyana abin da wannan sabuwar wayar ta Spark 8P dake ƙoƙarin zama – matsakaicin kudi.