Babban Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabuwar Na’urar Kyankyasa Jarirai

Kun ji? Wani masanin kimiya ya dan samu cigaba a aikin gina mahaifar wucin gadi inda za’a iya samar da jarirai 30,000 a cikin ta. An ce cigaba ne kan cigaban da masana kimiyya suka yi a wannan hanya a a shekarar 2017. Na’urar na ba iyaye damar su haifi jarirai na musamman.

Na fara samun alamar wannan, kamar yadda aka bayar da rahoton cewa shine “na farko a duniya” na irin wannan na’urar mai suna ‘Ectolife,’ daga wani faifan bidiyo da aka wallafa tare da bayanai masu firgitarwa:

“Muna kallon yadda waɗannan ‘yan duniya ke matsar da mu zuwa ga wani wuri mai mahimmanci, nan gaba inda za’a aiwatar da wani tsari na transhumanist, inda jinsi ya narke, inda ba a buƙatar mata masu ilimin halitta.

Bayanan ƙasidar ya ƙara da cewa, “Yau ƙamus na Cambridge ya sabunta ma’anar shi game da mata har ya haɗa da maza. Yanzu haka wani masanin ilmin kwayoyin halitta dan kasar Jamus ya bayyana wani sabon ra’ayi na ginin mahaifar wucin gadi na farko a duniya mai suna Ectolife wanda zai haifar da jarirai har 30,000 a shekara.”