Asalin Fulani Da Yadda Suka Kasance Wani Bangare Na Ƙabilun Najeriya

Fulani kabila ce ta makiyaya kuma daya daga cikin manyan kabilu a yankin Sahel da yammacin Afirka. Ana iya samun su a yawancin ƙasashen yammacin Afirka irin su Najeriya, Nijar, Guinea, Ghana, Mali, Senegal, da dai sauran su.

Duk da haka, a cikin labarin mu na yau, za mu bincika tarihin yadda Fulani suka shigo Najeriya, da yankin da suka yo hijira.

A cewar modernghana.com, yawancin masana tarihi sun yi imanin cewa Fulani sun samo asali ne daga mutanen Berber a Arewacin Afirka kafin su yo hijira zuwa yammacin Afirka a tsakanin karni na 8 zuwa na 11. Waɗannan mutanen Berber da suka yi ƙaura sun fara cuɗanya da mutanen Senegal kafin su bazu cikin yammacin Afirka.

A tsawon tarihin su, a karshe al’ummar Fulani sun zama kamar sun yi watsi da salon zaman su na makiyaya suna zama a kauyukan noma don noman shanu, kuma a yau an kiyasta cewa Fulani kusan miliyan 18 ne ke zaune a kasashen yammacin Afirka.

A yammacin Afirka, an yi imanin al’ummar Fulani ne suka fara shiga addinin Musulunci kasancewar kashi 99% na Musulmi ne. Bugu da kari, Fulani wadanda tun farko makiyaya ne suka zo Najeriya suka yi suna sakamakon koyarwar wani shahararren malamin Fulani mai suna Sheikh Usman Dan Fodio a farkon shekara ta 80.

Dan Fodio ya fara wa’azi akan sarakunan Hausawa na arewa, nan da nan ya dauki makami ya yaki wasu daga cikin wadannan masarautun Hausa, ya kafa daular Sokoto. Don haka wannan ya ba wa Fulani tuwo a kwarya da kwanciyar hankali a Nijeriya, suka zama wani bangare na al’ummar Nijeriya.