Amfanin Tafarnuwa Ga Namiji Wajen Jima’i

Cibiyar Kiwon Lafiya ta Jami’ar Rochester ta bayyana cewa tafarnuwa na dauke da sinadarin protein, fat, carbohydrates, fiber da muhimman ma’adanai kamar iron, calcium, potassium, phosphorus, potassium, vitamin B6 da C.

Tafarnuwa Na Ƙara Lafiyar Jima’i

Bincike ya gano cewa tafarnuwa na da sinadarin da ake kira Allicin wanda ke kara gudanar jini. Wannan na iya kara karfin azzakari da kara karfin sha’awar jima’i.

Maza suna iya cin tafarnuwa guda biyu zuwa uku kowace rana don cin moriyar tafarnuwa. Ana iya ci danye ko kuma a saka shi a abinci bayan an gasa shi.