Amfanin Tafarnuwa Ga Azzakari

A cewar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Jami’ar Rochester, tafarnuwa tana dauke da furotin, mai, carbohydrates, fiber da ma’adanai masu mahimmanci kamar iron, calcium, potassium, phosphorus, potassium, da bitamin B6 da C.

An san Tafarnuwa a matsayin babban abinci ga maza. Tana dauke da sinadirai masu yawa kamar magnesium, selenium da sauransu, wadanda zasu iya inganta lafiyar jima’i ta maza.

Bincike ya gano cewa tafarnuwa na da sinadarin da ake kira Allicin wanda ke kara habaka kwararar jini zuwa ga azzakari sosai. Wannan na iya kara karfin mazakuta da kara karfin sha’awar jima’i. Maza suna iya amfani tafarnuwa guda biyu zuwa uku kowace rana don cin moriyar tafarnuwa. Ana iya ci danye ko kuma a saka shi a abinci bayan an gasa shi.