Amfanin Magani Augurmentin

Augmentin wani maganin kwayoyin cututtuka ne da ake amfani da shi sosai don cututtukan ƙwayoyin cuta daban-daban.

Augmentin haɗe-haɗe ne na sinadarai masu aiki guda biyu, amoxicillin da clavulanic acid, waɗanda ke aiki tare don magance cututtukan da za su iya bijirewa wa amoxicillin shi kaɗai.

Augmentin yana da tasiri a kan nau’ikan cututtuka, ciki har da cututtuka na hanyoyin numfashi kamar; huhu maƙogaro, fata da cututtuka masu kanana, cututtuka na mafitsara, sanyi, tayifod da ciwon dodon kunne.

Wadannan faffadan ayyukan yana sa Augmentin ya zama kayan aiki mai mahimmanci kuma mai tasiri a cikin yaƙi da ƙwayoyin cuta, yana ba da taimako da warkarwa ga marasa lafiya da ke buƙata.