Lafiya

Amfanin Madarar Nonon Akuya Ga Jiki

Madarar nonon akuya babban tushen bitamin da sinadarai ne ga fata. A dabi’ance yana da yawan bitamin A, wanda ke taimakawa wajen kiyaye lafiyar fata, yayin da yake dauke da karin wata wasu kamar; bitamin B1, B6, B12, C, D da E.

Ya kuma ƙunshi muhimman sinadarai na ƙiba da sauran wasu sunadarai. Tsarin kwayoyin halitta na madarar akuya yana ba shi damar shiga cikin fata cikin sauƙi, yana ba ku damar cin gajiyar bitamin da sinadrai da ke cikinsa.

Bugu da ƙari, sinadarai na halitta a cikin madarar akuya yana taimakawa wajen lausasa fata, yana ba ta haske mai kyau.

Sabulun madarar akuya

Madarar akuya ba wadataccen bitamin da sinadarai kaɗai ta kunsa ba, har ila yau, madarar ita ce asalin tushen lactic acid ne, wanda ke taimakawa wajen kawar da matattun kwayoyin halitta na fata da rage alamun tsufa.

Wadannan Slsinadarai na halitta dake cikin madarar akuya suna taimakawa wajen bayyana fata mai laushi da haske.

Advertisement